Satin da ya wuce nayi wani gajeren rubutu akan Yan Majalisun Tarayya (Senators) su sittin da shida wanda suka raka Saraki zuwa CCT kuma bayan zabe…

Satin da ya wuce nayi wani gajeren rubutu akan Yan Majalisun Tarayya (Senators) su sittin da shida wanda suka raka Saraki zuwa CCT kuma bayan zabe adadin sittin da shida din suka fadi, ma’ana ba zasu dawo Majalisar ba sai wani abokina yayi comment da cewa suna ganin girmana saboda haka na daina irin wannan rubutu, wai ai tunda maganar zabe ne ai Buhari ya ci, ai shikenan.
Wannan comment ya daure mini kayi sosai. Su fa yan majalisan nan miliyoyin mutane ne suka zabe su don su je su kare musu mutuncinsu, su samo musu ayyukan raya mazabarsu, su kuma bi duk abunda suke so amma abun kunya sai su kayi biris suka watsar da jama’arsu suka kuma yi hannun riga da bukatun mazabar na su. Su ka je Abuja suka shantake suna karbar miliyoyin kudi basu ma tuna da jama’ar tasu ba balle su kawo musu ayyukan ci gaba.
To abokina ka tuna fa su yan majalisar nan sunyi rantsuwa da Al-Qur’ani cewa zasu yi aikin da aka zabe su saboda shi. Mai yasa ba zaka ce musu su duba Girman Allah wanda suka yi rantsuwa da Shi su gyara halayensu ba? Mai yasa ba zaka tunasar dasu cewa nauyi suka dauka na wakiltar jama’arsu ba? Mai yasa ba zaka tunasar dasu cewa Allah zai musu tambaya akan yanda suka tafiyarda wakilcin jama’a da suka dauka ba?
Zaben Buhari ba shine karshen siyasar 2019 ba, dole sai mun kushe na kushewa saboda kar a sake zaben tumun dare a cikin yan tafiyar. Shi da kansa Buhari na sha kushe shi akan abubuwa da dama kamar akan rashin tsaro a Zamfara, rashin zuwa jajen yan matan da aka sace a Dapchi da wuri da wasu kura-kurai da dama.
To ka ga dole na kushe mutanen da suka je Abuja suka yi ta sharholiyarsu har na tsawon shekara hudu basu tabukawa Nigeria da kuma al’ummarsu da komai ba.


Facebook: https://www.facebook.com/bulama.adamu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *