Dadin Kowa , Sabuwa tace wa Dan Asabe ba don ku ba, da na jima da barin gidan nan

Dadin Kowa
Sabuwa tace wa Dan Asabe ba don ku ba, da na jima da barin gidan nan. Wannan shine halinda wasu mata suke ciki a gidajen mazajensu. Suna zaune ne saboda gudun kar su fita yaran su shiga wani hali musamman ma idan aka kawo musu muguwar mace a matsayin Babarsu.
Ya kamata masu muzgunawa mata suji tsoron Allah su daina. Su sani cewa Allah zai tambayesu yanda suka tafiyar da zamantakewarsu. Ka zama mai kyautatawa da farantawa matarka hakan zai kawo karin kauna, fahimtar juna da kuma samun walwala da farin ciki a cikin gidanka.
Sabuwa ta cewa Mallam Ayuba ‘My Dear zanje anguwa.’ A nanne ma gizo yake sakar. Mata suna zaune ne ba wani kisisina in kuma har kaji ana yi to lallai dayan biyu: ko zata anguwa ko kuwa tana bukatar yan sulalla. To kuma ku daina irin wannan. Ku dinga kwalliya da dadadan kalamu ba sai zaku je anguwa ba. Sai kuce wai Arewa men are not romantic, to ku dinfa? Kowa ya gyara dan al’amura su yi kyau


Facebook: https://www.facebook.com/bulama.adamu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *